Jeremiah 51:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da ya yi tsawa ruwan da suke sammai sukan yi ruri; yakan sa gizagizai su tashi daga ƙarshen duniya. Yakan tura walƙiya tare da ruwan sama yakan kuma saki iska daga cikin taskokinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَجِنْ مُرْيَرْسَ، ضُوَيٜىٰنْ سَمَ سُكَنْيِ رُورِ؞ يَكَنْ تَادَ غِذَغِظَيْ دَغَ إِيَاكَرْ دُونِيَا، يَكَنْ عَيْكُواْ دَ وَلْڧِيَ تَرٜىٰدَ ضُوً سَمَ، يَكَنْ كُمَ ڢِتَرْدَ إِسْكَ دَغَ طَاكِنْ أَجِيَرْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bisa ga umarninsa ruwan da yake samaniya yakan yi ruri, Yakan sa gajimare su tashi daga ƙarshen duniya, Yakan sa walƙiya ta walƙata cikin ruwan sama, Yakan sa iska ta haura daga cikin taskokinsa.