Jeremiah 51:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ga shi, ina gāba da kai, ya ke dutse mai hallakarwa, wadda ta hallaka duniya duka,” in ji Ubangiji. “Zan miƙa hannuna gāba da ke, zan mirgina ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, zan maishe ki ƙonannen dutse.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَاشِ، يَا كٜىٰ بَابِيلَ، بَبَّنْ دُواْدُواْ مَيْ هَلَّكَرْوَ، مَيْ هَلَّكَرْ دَ دُكَنْ دُونِيَا، ذَنْ مِيڧَ هَنُّونَ نَغَابَادَكٜىٰ، ذَنْ تُورَكِ كِغَنْ‌غَرَ دَغَ سَمَنْ تُدُ حَرْ ڧَسَا، ذَنْ ڧُواْنٜىٰكِ كِذَمَ تُلِنْ تُواْكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga shi, ina gaba da kai, ya dutse mai hallakarwa, Wanda ya hallaka duniya duka. Zan miƙa hannuna gāba da kai, Zan mirgino da ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, Zan maishe ka ƙonannen dutse.