Jeremiah 51:34 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Nebukadnezzar sarkin Babilon ya cinye mu, ya sa muka rikice, ya maishe mu kamar tulun da babu kome a cikinsa. Ya cinye mu kamar yadda dodon ruwa yakan yi ya kuma cika cikinsa da kayan marmarinmu, sa’an nan kuma ya yi amanmu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ عُرُوشَلِيمَ سُنْثٜىٰ، «سَرْكِے نٜىٰبُكَدْنٜىٰزَّرْ يَثِنْيٜىٰمُ، يَمُرْڧُشٜىٰمُ، يَهَطِيٜىٰمُ كَمَرْ يَدَّ دُواْدُوانْ ضُوَ يَكَنْيِ، يَثِكَ ثِكِنْسَ دَ عَبِنْثِ مَيْ دَاطِے؞ يَبَرْ تُكُنْيَ مَرَرْ كُواْمٜىٰ، يَوَنْكٜىٰ تُكُنْيَرْ سَرَيْ يَظُبَرْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya cinye Urushalima, Ya ragargaza ta, Ya maishe ta kufai, Ya haɗiye ta kamar yadda dodon ruwa yakan yi, Ya cika cikinsa da kayan marmarinta, Ya tatse ta sarai.