Jeremiah 51:47 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gama kwanaki tabbatacce suna zuwa, sa’ad da zan hukunta gumakan Babilon, zan kunyatar da dukan ƙasar kuma matattunta duk za su kwanta a cikinta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«حَڧِيڧَ، ݣُونَكِے سُنَ ذُوَا عِنْدَ ذَنْ حُكُنْتَ غُمَكَنْ بَابِيلَ؞ دُكَنْ ڧَسَرْ بَابِيلَ، ذَاعَ كُنْيَتَرْ دَ عِتَ، مُتَنٜىٰنْتَ ذَاسُ ݣُونْتَ مَتَتُّو كُواْعِنَ عَڧَسَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda haka kwanaki suna zuwa, Sa'ad da zan hukunta gumakan Babila, Za a kunyatar da dukan ƙasar Babila, Dukan matattunta za su faɗi a tsakiyarta.