Jeremiah 51:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Babilon ta zama ƙoƙon zinariya a hannun Ubangiji, ta sa dukan duniya ta yi maye. Ƙasashe sun sha ruwan inabinta, saboda haka yanzu sun haukace.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ دَا بَابِيلَ كَمَرْ ݣُوڢْ نَظِينَارِيَثٜىٰ أَ هَنُّونَ، نِے يَهْوٜىٰهْ ؞ تَا سَا دُكَنْ دُونِيَا تَبُغُ، أَلْعُمَّنْ دُونِيَا سُنْ شَا ضُوً إِنَبِنْتَ سُكَ هَوْكَثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Babila ta zama ƙoƙon zinariya a hannun Ubangiji, Ta sa dukan duniya ta yi maye. Ƙasashen duniya sun sha ruwan inabinta, suka haukace.