Jeremiah 51:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Farat ɗaya Babilon za tă fāɗi ta farfashe. Ku yi kuka dominta! Ku samo mata magani saboda azabarta; wataƙila za a iya warkar da ita.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَا لَابَرِ بَابِيلَ تَڢَاطِ تَكَكَّرْيٜىٰ، كُيِ كُوكَا دُواْمِنْتَ! كُسَامُواْ مَتَ مَاغَنِ دُواْمِنْ رَوْنِنْتَ، وَتَڧِيلَ ذَاتَوَرْكٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Farat ɗaya, Babila ta fāɗi, ta kakkarye, Ku yi kuka dominta! Ku samo mata magani domin azabar da take sha, watakila ta warke.