Jeremiah 52:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babilon, da sauran masu sana’a, ya kai su bautar talala a Babilon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً نٜىٰبُظَرَدَنْ يَݣُوشِ ضَغُواْوَرْ جَمَعَ دَغَ عُرُوشَلِيمَ ذُوَا ذَمَنْ بَوْتَادَ كُمَ وَطَنْسُ مَڢِے تَلَوْثِ دَ وَطَنْدَ دَا سُكَ غُدُ سُكَ بَادَ كَنْسُ أَ حَنُّنْسَ دَ وَطَنْسُ مَاسُ سَنَعَرْ حَنُّ وَطَنْدَ سُكَ ضَغٜىٰ، دُكَنْسُ يَكَيْسُ ذَمَنْ بَوْتَا عَ بَابِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Nebuzaradan shugaban matsara ya kwashe waɗansu matalauta, da sauran mutane da aka bari a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran masu sana'a, ya kai su bautar talala a Babila.