Jeremiah 6:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ki ji, ya duniya. Zan kawo masifa a kan waɗannan mutane, sakayyar ƙulle-ƙullensu, domin ba su saurari maganata ba suka kuma ƙi dokata.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَا كٜىٰ دُونِيَا، كِكَسَ كُنّٜىٰ! غَاشِ، نِے ذَنْ كَٰوُاْ مَسِيڢَ عَكَنْ جَمَعَرْ نَنْ، سَكَمَكُوانْ ڧُلّٜىٰ ڧُلّٜىٰنْسُ، غَمَا بَسُ كَسَ كُنّٜىٰ غَ مَغَنَاتَبَ، كُواْيَرْوَاتَا كُوَ سُنْڧِے سُبِيتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ki ji, ya ke duniya, Ga shi, ina kawo masifa a kan wannan jama'a, Sakayyar ƙulle-ƙullensu, Don ba su kula da maganata ba, Sun ƙi dokokina.