Jeremiah 6:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “Zan sa abin tuntuɓe gaban mutanena. Mahaifi da ’ya’yansa maza za su yi tuntuɓe a kan juna; maƙwabci da abokansa za su hallaka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ «سَبُواْدَ حَكَ، غَاشِ، ذَنْسَا أَبِنْ تُنْتُنْٻٜىٰ أَغَبَنْ جَمَعَرْ نَنْ، وَنْدَ ذَاسُيِ تُنْتُٻٜىٰ عَكَيْ؞ إِيَايٜىٰ دَ یَیَ، مَڨُوبْتَ دَ أَبُواْكَيْ، دُكَ ذَاسُ هَلَّكَ تَرٜىٰ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don haka, ni Ubangiji na ce, Zan sa abin tuntuɓe a gaban wannan jama'a, Za su kuwa yi tuntuɓe, su fāɗi. Iyaye tare da 'ya'yansu, da maƙwabci, Do abokansu za su lalace.”