Jeremiah 7:31 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sun gida masujadan Tofet a Kwarin Ben Hinnom don miƙa ’ya’yansu maza da mata a wuta, abin da ban yi umarni ba, ba kuwa yi tunaninsa ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُنْ غِنَا وُرَارٜىٰنْ سُجَّدَ نَ تُواْڢٜىٰتْ أَ ݣُورِنْ طَنْ هِنُّوامْ، دُواْمِنْ سُڧُواْنَ یَیَنْسُ مَظَا دَ مَاتَا عَثِكِنْ وُتَرْ؞ نِے كُوَ بَنْ عُمَرْثٜىٰسُ سُيِ حَكَبَ، بَنْ مَا يِتُنَانِنْ إِرِنْ وَنَّنْ أَبُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A cikin kwarin ɗan Hinnon sun gina bagade, mai suna Tofet, don su miƙa 'ya'yansu mata da maza hadayar ƙonawa. Ni ban umarce su su yi haka ba, irin wannan abu ba shi a zuciyata.