Jeremiah 7:32 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka ku yi hankali, kwanaki suna zuwa in ji Ubangiji, sa’ad da mutane ba za su ƙara kira wurin Tofet ko Kwarin Ben Hinnom ba, amma Kwarin Kisa, gama za su binne matattu a Tofet sai har ba sauran wuri.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُواْمِنْ حَكَ، غَاشِ ݣُونَكِے سُنَ ذُوَا، لُواْكَثِنْ دَ بَذَاعَ ڧَارَ كِرَا وُرِنَّنْ تُواْڢٜىٰتْ كُواْ ݣُورِنْ طَنْ هِنُّوامْ بَ، عَمَّا ذَاعَ كِرَشِ ݣُورِنْ كِسَ؞ غَمَا ذَاعَ بِنّٜىٰ مُتَنٜىٰ أَ تُواْڢٜىٰتْ حَرْ سَيْ وُرِنْ بِنّٜىٰوَ يَكَاسَ؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Domin haka, ni Ubangiji na ce, kwanaki suna zuwa lokacin da ba za a ƙara faɗar Tofet, ko kwarin ɗan Hinnom ba, amma za a kira shi Kwarin Kisa, gama za a binne mutane a Tofet domin ba sauran wuri a ko'ina.