Jeremiah 7:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Za ku yi sata da kisa, ku yi zina da rantsuwar ƙarya, kuna ƙone turare wa Ba’al kuna kuma bin waɗansu allolin da ba ku sani ba,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَاشِ، كُنْيِتَيِنْ سَاتَادَ كَشٜىٰ كَشٜىٰ دَ ظِنَ دَ ضَنْڟُوَارْ ڧَضْيَا دَ ڧُواْنَاوَا غُنْكِنَّنْ بَعَلْ تُرَارٜىٰ دَ بِنْ وَطَنْسُ أَلُّواْلِنْ دَ دَا بَكُسَنِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za ku yi ta yin sata, da kisankai, da zina, da rantsuwar ƙarya, da ƙona wa Ba'al turare, da bin waɗansu gumakan da ba ku sani ba?