Jeremiah 8:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘A wancan lokaci, in ji Ubangiji, za a fitar da ƙasusuwan sarakuna da na shugabannin Yahuda, ƙasusuwan firistoci da na annabawa, da kuma ƙasusuwan mutanen Urushalima daga kaburbura.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ « ‹أَ لُواْكَثِنَّنْ، ذَاعَ ڢِتَرْدَ ڧَسُسُوَنْ سَرَاكُنَنْ يَهُودَ دَ نَدَتَّوَنْسُ دَ نَڢِرِسْتُواْثِے دَ نَأَنَّبَوَ دَ نَمَذَوْنَنْ عُرُوشَلِيمَ دَغَ كَبُرْبُرَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ni Ubangiji na faɗa, cewa a wancan lokaci, za a fitar da ƙasusuwa daga kaburburan sarakunan Yahuza, da na sarakansu, da na firistoci, da na annabawa, da na mazaunan Urushalima.