Jeremiah 8:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sukan ji kunyar halin banƙyamarsu kuwa? Sam, ba su da kunya ko kaɗan; ba su ma san yadda za su ji kunya ba. Saboda haka sukan fāɗi tare da fāɗaɗɗu; za su fāɗi sa’ad da aka hukunta su, in ji Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُنْيِ أَبِنْ كُنْيَا، سُنْ عَيْكَتَ أَبُبُوَنْ بَنْ ڨَمَ، عَمَّا بَسُجِ كُنْيَا بَ كُواْ كَطَنْ؞ بَسُ مَا سَنْ يَدَّ ذَاعَ سُنْكُيَرْ دَكَيْ ثِكِنْ كُنْيَابَ؞ سَبُواْدَ حَكَ، ذَاسُ ڢَاطِ عَثِكِنْ مَاسُ ڢَاطُوَ، سَعَدَّ نَحُكُنْتَسُ، ذَاعَ تُمْٻُكٜىٰسُ؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ko sun ji kunya Sa'ad da suka aikata ayyuka masu banƙyama? A'a, ba su ji kunya ba ko kaɗan, Fuskarsu ko gezau ba ta yi ba. Domin haka za su faɗi tare da fāɗaɗɗu, Sa'ad da na hukunta su, za a ci su da yaƙi. Ni Ubangiji na faɗa.’