Jeremiah 8:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ko shamuwa ta sararin sama ma takan san lokutan da aka tsara mata, kurciya, mashirare da kuma zalɓe sukan lura da lokacin ƙauransu. Amma mutanena ba su san abubuwan da Ubangiji yake bukata ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْ شَمُوَ تَسَرَرِنْ سَمَ مَا، تَسَنْ ڧَٰعِدَرْ لُواْكَتَنْ ڧَوْرَرْتَ؞ تَتَّبَرَ دَ ڟَڟّٜىٰوَ دَ ظَلْٻٜىٰ، سُنَ كِيَايٜىٰ لُواْكَثِنْ كُواْمُواْوَرْسُ؞ عَمَّا جَمَعَتَ، بَسُ سَنْ حَكَبَ، بَسُسَنْ ڧَٰعِدَرْ دَ نِے يَهْوٜىٰهْ نَكَڢَ مُسُبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ko shamuwa ta sararin sama ma, ta san lokatanta, Tattabara da tsattsewa, da gauraka suna kiyaye lokacin komowarsu. Amma mutanena ba su san dokokina ba.