Jeremiah 9:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wane mutum ne yana da isashiyar hikimar fahimtar wannan? Wa Ubangiji ya umarta da zai iya yin bayani? Me ya sa aka lalace ƙasar ta zama kufai kamar hamada da ba wanda zai iya ratsa ta?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نِے إِرْمِيَ نَيِ تَمْبَيَ نَثٜىٰ «دُوانْمٜىٰ ڧَسَرْ تَبُوشٜىٰ تَذَمَ كُڢَيْ كَمَرْ دَاجِ، حَرْ بَابُ مَيْ تَڢِيَ عَثِكِنْتَ؟ وَنٜىٰنٜىٰ يَكٜىٰدَ حِكِمَرْ دَ ذَيْ عِيَ غَانٜىٰ وَنَّنْ؟ وَنٜىٰنٜىٰ يَهْوٜىٰهْ يَڢَطَا مَسَ دُواْمِنْ يَبَيَّنَ وَمُتَنٜىٰ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wa yake da isasshiyar hikimar da zai fahimci wannan? Wa Ubangiji ya faɗa masa don ya sanar? Me ya sa ƙasar ta lalace ta zama kufai, har ba wanda yake iya ratsa ta, kamar hamada?