Jeremiah 9:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutuwa ta haura ta tagoginmu ta kuma shiga katangarmu; ta karkashe ’ya’ya a tituna ta kuma karkashe samari a dandali.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا مُتُوَ تَا شِغَ مَنَ تَتَغَ، تَا شِغَ ثِكِنْ وُرَارٜىٰنْمُ مَاسُ كَتَنْ‌غَ، تَا كَوَرْدَ یَیَ دَغَ تِيتُنَ، سَمَارِنْمُ كُمَ دَغَ ڢِيلِ نَثِكِنْ غَرِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama mutuwa ta shiga tagoginmu, Ta shiga cikin fādodinmu, Ta karkashe yara a tituna, Ta kuma karkashe samari a dandali.