Jeremiah 9:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ka ce, “Ga abin da Ubangiji ya furta, “ ‘Gawawwakin mutane za su fāɗi kamar juji a fili, kamar hatsin da aka yanka a bayan mai girbi, da ba mai tara su.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ «كَيِ مَغَنَ ثٜىٰوَ « ‹غَوَوَّكِنْ مُتَنٜىٰ ذَاسُ ڢَاطِ ذَاعَ تَتَّاكَ كَمَرْ كَاشِنْ دَبَّ أَ ڢِيلِنْ غُواْنَ، كَمَرْ دَمِ دَمٍ حَڟِ بَايَنْ مَيْ غِرْبِے يَيِ عَيْكِ، كُمَ بَابُ مَيْ تَتَّرَاوَا؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya ce mini, ‘Ka yi magana, cewa gawawwakin mutane za su fāɗi tuli Kamar juji a saura, Kamar dammunan da masu girbi suka ɗaura, Ba wanda zai tattara su.’ ”