Job 1:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
’Ya’yansa maza sukan yi biki a gidajensu, wannan yă yi yă ba wancan, sai su kira ’yan’uwansu mata ukun su ci, su sha tare.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
یَیَنْسَ مَظَا سُكَنْيِ بِكِ بِيدَبِے عَثِكِنْ غِدَاجٜىٰنْ جُونَنْسُ، سُكَنْ كُمَ غَيَّثِ یَنْعُوَنْسُ مَتَ غُدَا عُكُنَّنْ سُثِ سُشَا تَرٜىٰدَسُو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
'Ya'yansa maza sukan yi liyafa bi da bi a gidajen junansu, inda su duka sukan taru koyaushe, sukan gayyaci 'yan'uwan nan nasu mata su halarci liyafar.