Job 1:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan lokacin bikin ya wuce, sai Ayuba yă aika su zo don yă tsarkake su. Tun da sassafe zai miƙa hadaya ta ƙonawa domin kowannensu, don yana tunani cewa, “Mai yiwuwa ’ya’yana sun yi wa Allah zunubi, ko sun la’anta shi a cikin zuciyarsu.” Haka Ayuba ya saba yi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ ݣُونَكِنْ بِكٍ سُنْ ڧَارٜىٰ، أَيُوبَ يَكَنْ كِرَا يَسَا أَڟَرْكَكٜىٰسُ؞ وَشٜىٰغَرِ دَ سَسَّڢٜىٰ شِے ذَيْ مِيڧَ هَدَايُ نَڧُواْنَاوَا دُواْمِنْ كُواْوَنٜىٰ طَيَنْسُ؞ غَمَا أَيُوبَ يَكَنْيِ ظَتُواْ ثٜىٰوَ «وَتَڧِيلَ یَیَنَ سُنْيِ ذُنُوبِ، كُواْ سُنْيِ صَاٻُواْ غَ اللَّهْ عَثِكِنْ ذُوثِيَارْسُ؞» حَكَ أَيُوبَ يَكَنْيِ كُلُّمْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A kowane lokacin da aka gama da liyafar, Ayuba yakan tashi da sassafe, kashegarin liyafar, yă miƙa hadayu don yă tsarkake 'ya'yansa. Haka yake yi kullum, don yana zaton mai yiwuwa ne ɗaya daga cikin 'ya'yan ya yi zunubi, ya saɓi Allah a ɓoye.