Job 24:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗanda suka haife su za su manta da su, tsutsotsi za su cinye su; ba za a sāke tunawa da mugaye ba amma an sare su kamar itace.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَامَرْ دَ تَحَيْڢٜىٰشِ ذَاتَ مَنْتَادَشِ، ڟُڟَ ذَاتَ جِ دَاطِنْ ثِنْيٜىٰ جِكِنْسَ، بَاوَنْدَ ذَيْ ڧَارَ تُنَ دَشِ، حَكَ ذَاعَ كَرْيَ رَشِنْ غَسْكِيَ كَمَرْ إِتَاثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba wanda zai tuna da shi, mahaifiyarsa ma ba za ta lura da shi ba. Tsutotsi sukan ci shi su hallaka shi sarai. Za a sare mugunta kamar itace.