Job 42:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dukan ’yan’uwansa maza da mata da duk waɗanda suka san shi a dā suka zo suka ci abinci tare da shi a cikin gidansa. Suka ta’azantar da shi suka ƙarfafa shi game da duk wahalar da Ubangiji ya auka masa, kowannensu kuma ya ba shi azurfa da zobe na zinariya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً دُكَنْ یَنْعُوَنْ أَيُوبَ مَاتَادَ مَظَا دَ دُكَنْ وَطَنْدَ سُكَ سَنْ شِ أَدَا، سُكَذُواْ غِدَنْسَ سُكَثِ سُكَشَا تَرٜىٰ؞ سُكَ تَوْسَيَ مَسَ دَ أَبِنْدَ يَڢَرُ دَشِ، سُكَ كُمَ تَعَظَنْتَرْ دَشِ سَبُواْدَ دُكَنْ وَهَلَرْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَجَٰوُاْ عَكَنْسَ؞ كُواْوَنّٜىٰنْسُ كُمَ يَبَا أَيُوبَ كُطِ دَ ذُواْبٜىٰ نَظِينَارِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan dukan 'yan'uwan Ayuba mata da maza da dukan waɗanda suka san shi a dā, suka zo gidansa suka ci abinci tare da shi, suka yi juyayin abin da ya same shi, suka ta'azantar da shi,saboda dukan wahalar da Ubangiji ya aukar masa. Kowannensu ya ba shi 'yan kuɗi da zoben zinariya.