Joel 1:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kuringar inabin ta bushe itacen ɓaure kuma ya yi yaushi, ’ya’yan rumman, itacen dabino da itacen gawasa, dukan itatuwan filaye, sun bushe. Tabbatacce farin cikin ’yan adam ya bushe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غُواْنَكِنْ إِنَبِے سُنْ بُوشٜىٰ كَكَڢْ! عِتَتُوَنْ ٻَوْرٜىٰ دُكْ سُنْ بُوشٜىٰ، حَكَمَا إِتَاثٜىٰنْ رُمَّنْ، دَ نَڨُورَ دَ نَیَیَنْ إِتَاثٜىٰ مَاسُ ذَاڧِ، دُكَنْ عِتَتُوَنْ غُواْنَكِ سُنْ بُوشٜىٰ، بَاشَكَّ، ڢَضٍ ثِكِ يَبُوشٜىٰ سَرَيْ دَغَ یَنْ أَدَمْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kurangar inabi ta bushe, Itatuwan ɓaure kuma sun yi yaushi, Rumman, da dabino, da gawasa, Da dukan itatuwan gonaki sun bushe. Murna ta ƙare a wurin mutane.