John 11:28 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan ta faɗa haka kuwa, sai ta koma ta je ta kira ’yar’uwarta Maryamu a gefe. Ta ce, “Ga Malam ya zo, kuma yana kiranki.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ تَڢَطِ حَكَ، سَيْ تَجٜىٰ تَكِرَوُاْ یَرْعُوَرْتَ مَرْيَمُ، تَثٜىٰ «مَلَمْ يَاذُواْ، كُمَ يَنَ كِرَنْكِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da ta faɗi haka, ta je ta kirawo 'yar'uwa tata Maryamu, ta raɗa mata ta ce, “Ga Malam ya zo, yana kiranki.”