John 11:44 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a daure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi. Yesu ya ce musu, “Ku tuɓe kayan bizo, ku bar shi yă tafi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مُتُمِنْدَ يَمُتُ طِنْ يَڢِتُواْ، ڧَڢَا دَ حَنُّ أَطَوْرٜىٰ دَ غُنْتَيٜىٰنْ يَدِ، ڢُسْكَرْسَ كُمَ أَ نَطٜىٰ تَكٜىٰدَ ذَنٜىٰنْ دَ عَكَ بِنّٜىٰشِ دَشِ؞ سَيْ عِيسَىٰ يَثٜىٰ مُسُ «كُكُنْثٜىٰشِ، يَتَڢِے؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai mamacin ya fito, ƙafa da hannu a ɗaure da likkafani, fuska tasa kuma a naɗe da mayani. Yesu ya ce musu, “Ku kwance masa, ya tafi.”