John 11:47 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai manyan firistoci da Farisiyawa suka kira taron Majalisa. Suka yi tambaya suna cewa, “Me muke yi ne? Ga mutumin nan yana yin abubuwan banmamaki masu yawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُواْمِنْ حَكَ مَنْيَنْ ڢِرِسْتُواْثِے دَ ڢَرِسِيَاوَا سُكَ تَارَ یَنْ مَجَلِسَ؞ سُكَ تَمْبَيِ جُونَ سُكَثٜىٰ «مٜىٰ مُكٜىٰيِ نٜىٰ؟ غَا وَنَّنْ مُتُمِنْ يَنَ يِنْ عَلَمُنْ بَنْ مَامَاكِ دَيَوَ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don haka manyan firistoci da Farisiyawa suka tara 'yan majalisa, suka ce, “Shin, me muke yi ne, har mutumin nan yake ta yin mu'ujizai da yawa haka?