John 11:54 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba. A maimako haka sai ya janye zuwa yankin kusa da hamada, a wani ƙauye da ake kira Efraim, inda ya zauna da almajiransa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ عِيسَىٰ بَيْ ڧَارَ تَڢِيَ ثِكِنْ يَهُودَاوَا أَ ڢِيلِ بَ، عَمَّا يَبَرْ وُرِنْ، يَتَڢِے ڧَسَرْدَ تَكٜىٰ كُسَدَ دَاجِ، يَشِغَ وَنِ غَرِ مَيْ سُونَ إِڢْرَيِمْ؞ أَ نَنْ نٜىٰ يَذَوْنَ دَ أَلْمَجِرَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda haka, Yesu bai ƙara tafiya a cikin Yahudawa a sarari ba, amma ya tashi daga wurin, ya tafi ƙasar da take a bakin jeji, ya shiga wani gari, mai suna Ifraimu. Nan ya zauna da almajiran.