John 13:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan Yesu ya faɗi haka, sai ya yi juyayi a ruhu, ya kuma furta cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْدَ عِيسَىٰ يَيِ وَنَّنْ مَغَنَ، أَبِنْ يَدَامٜىٰشِ سُواْسَيْ أَ ذُوثِيَا؞ سَيْ يَڢَطَا أَ ڢِيلِ ثٜىٰوَ «غَسْكِيَ، إِنَ غَيَ مُكُ، طَيَنْكُ ذَيْبَاشٜىٰنِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan da Yesu ya faɗi haka, ya ji nauyi a ransa, ya yi shaida ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bāshe ni.”