John 14:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gaskiya nake gaya muku, duk wanda yake da bangaskiya gare ni, zai yi abubuwan da ni nake yi. Zai ma yi abubuwa masu girma fiye da waɗannan, don zan tafi wurin Uba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَڧِيڧَ، إِنَ غَيَ مُكُ، دُكْ وَنْدَ يَكٜىٰ بَادَ غَسْكِيَ غَرٜىٰنِ، ذَيْ يِ أَيُّكَنْ دَ نَكٜىٰيِ؞ حَرْ مَا ذَيْ يِ أَيُّكَنْ دَ سُكَڢِے وَطَنَّنْ، دُواْمِنْ ذَنْتَڢِے وُرِنْ عُبَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Lalle hakika, ina gaya muku, duk wanda yake gaskatawa da ni ayyukan da nake yi shi ma haka zai yi. Har ma, zai yi ayyukan da suka fi waɗannan, domin zan tafi wurin Uba.