John 14:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk wanda yake da umarnaina yana kuma yin biyayya da su, shi ne wanda yake ƙaunata. Wanda yake ƙaunata kuwa Ubana zai ƙaunace shi, ni ma zan ƙaunace shi, in kuma bayyana kaina gare shi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ وَنْدَ يَسَنْ عُمَرْنَيْنَ، يَنَ بِنْسُ كُمَ، شِينٜىٰ يَكٜىٰ ڧَوْنَتَ؞ وَنْدَ يَڧَوْنَثٜىٰنِ كُوَ، عُبَانَ ذَيْ ڧَوْنَثٜىٰشِ، نِے كُمَ ذَنْ ڧَوْنَثٜىٰشِ إِنْبَيَّنَ كَيْنَ أَغَرٜىٰشِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Duk wanda ya san umarnaina, yake kuma binsu, shi ne mai ƙaunata. Mai ƙaunata kuwa, Ubana zai ƙaunace shi, ni kuma zan ƙaunace shi, in bayyana kaina gare shi.”