John 14:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wanda ba ya ƙaunata ba zai yi biyayya da koyarwata ba. Waɗannan kalmomin da kuke ji ba nawa ba ne; na Uba ne da ya aiko ni.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنْدَ بَايَ ڧَوْنَتَ كُوَ، بَايَ كِيَايٜىٰ مَغَنَاتَ؞ مَغَنَرْ دَ كُكٜىٰجِ كُوَ بَتَوَ بَثٜىٰ، تَ عُبَا ثٜىٰ وَنْدَ يَأَيْكُواْنِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wanda ba ya ƙaunata, ba ya kiyaye maganata. Maganar da kuke ji kuwa ba tawa ba ce, ta Uba ce wanda ya aiko ni.