John 14:28 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Kun dai ji na ce, ‘Zan tafi in kuma sāke dawo wurinku.’ In har kuna ƙaunata, za ku yi farin ciki cewa za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«كُنْ دَيْجِ نَثٜىٰمُكُ ذَنْتَڢِے، إِنْسَاكٜىٰ دَاوُاْوَ وُرِنْكُ كُمَ؞ دَاكُنَ ڧَوْنَتَ دَا كُنْيِ مُرْنَ سَبُواْدَ ذَانِ وُرِنْ عُبَا، غَمَا عُبَنْ يَڢِينِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kun dai ji na ce muku zan tafi, in kuma dawo wurinku. Da kuna ƙaunata da kun yi murna saboda za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni.