John 18:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da ya gama addu’a, sai Yesu ya fita tare da almajiransa suka haye Kwarin Kidron. A wancan ƙetaren kuwa akwai lambun zaitun, da shi da almajiransa suka shiga ciki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْدَ عِيسَىٰ يَغَمَ وَنَّنْ أَدُّعَ، سَيْ يَڧٜىٰتَرٜىٰ رَاڢِنْ كِدْرُوانْ ذُوَا وَنْثَنْ ڧٜىٰتَرٜىٰ تَرٜىٰدَ أَلْمَجِرَنْسَ؞ عَڧٜىٰتَرٜىٰنْ رَاڢِنْ كُوَ أَݣَويْ وَتَ غُواْنَ، سَيْ عِيسَىٰ دَ أَلْمَجِرَنْسَ سُكَ شِغَ ثِكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan Yesu ya yi maganan nan, ya fita, shi da almajiransa zuwa hayin Rafin Kidron, inda wani lambu yake, ya kuma shiga da almajiransa.