John 18:37 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Bilatus ya ce, “To, wato, kai sarki ne!” Yesu ya amsa ya ce, “Haka yake, ni sarki ne yadda ka faɗa. Tabbatacce, saboda wannan dalili ne aka haife ni, kuma don wannan ne na zo duniya, domin in shaidi gaskiya. Duk wanda yake gefen gaskiya yakan saurare ni.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ بِلَتُسْ يَثٜىٰ «أَشٜىٰ، كَيْ سَرْكِے نٜىٰ؟» عِيسَىٰ يَأَمْسَ مَسَ يَثٜىٰ «كَيْ نٜىٰ دَكَنْكَ كَثٜىٰ نِے سَرْكِے نٜىٰ؞ وَنَّنْ شِينٜىٰ دَلِيلِنْ دَ عَكَ حَيْڢٜىٰنِ، شِينٜىٰ كُمَ دَلِيلِنْدَ نَشِغُواْ دُونِيَا، دُواْمِنْ إِنْبَادَ شَيْدَ غَ غَسْكِيَ؞ كُمَ دُكْ وَنْدَ يَكٜىٰ نَغَسْكِيَ، يَكَنْ سَوْرَرِ مُرْيَتَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Bilatus ya ce masa, “Wato ashe, sarki ne kai?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗa, ni sarki ne. Domin haka musamman aka haife ni, don haka kuma musamman na shigo duniya, domin in shaidi gaskiya. Kowane mai ƙaunar gaskiya kuwa yakan saurari muryata.”