John 19:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da sojojin suka gicciye Yesu, sai suka ɗibi tufafinsa suka kasa kashi huɗu, kowanne ya ɗauki kashi ɗaya. Suka kuma ɗauki taguwarsa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta daga sama har ƙasa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْدَ سُواْجُواْجِنْ سُكَ غِثِّيٜىٰ عِيسَىٰ ، سُكَ طِبِے تُڢَاڢِنْسَ، سُكَ رَبَ كَشِ حُطُ، كُواْوَنّٜىٰ سُواْجَ يَطَوْكِ كَشِ طَيَ؞ سُنْ كُمَ طَوْكِ دُواْغُوَرْ رِغَرْسَ وَدَّ بَعَطِنْكَ تَبَ، عَمَّا أَنْسَاڧَتَ نٜىٰ تُنْدَغَ سَمَ حَرْ ذُوَا ڧَسَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan soja sun gicciye Yesu, suka ɗibi tufafinsa, suka kasa kashi huɗu, kowane soja ya ɗauki kashi guda. Suka kuma ɗauki taguwa tasa, taguwar kuwa ba ɗinki, saƙa ɗaya ce gudanta.