John 19:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Nan da nan da manyan firistoci da ma’aikatansu suka gan shi, sai suka yi ihu suka ce, “A gicciye! A gicciye!” Amma Bilatus ya amsa ya ce, “Ku, ku ɗauke shi ku gicciye. Ni dai ban same shi da wani abin zargi ba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ مَنْيَنْ ڢِرِسْتُواْثِے دَ مَاسُ غَادِنْ هَيْكَلِ سُكَغَ عِيسَىٰ ، سَيْ سُكَيِ إِيهُ سُنَ ثٜىٰوَ «أَغِثِّيٜىٰشِ! أَغِثِّيٜىٰشِ!» عَمَّا بِلَتُسْ يَثٜىٰ مُسُ «كُجٜىٰ كُغِثِّيٜىٰشِ دَ كَنْكُ، دُواْمِنْ نِے بَنْ سَامٜىٰشِ دَ وَنِ لَيْڢِے بَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da manyan firistoci da dogaran Haikali suka gan shi, suka ɗau kururuwa suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi ku da kanku, ku gicciye shi, ni kam, ban same shi da wani laifi ba.”