John 20:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ya ce, “Mace, don me kike kuka? Wa kike nema?” Ta yi tsammani shi ne mai aikin lambun, sai ta ce, “Ranka yă daɗe, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka ajiye shi, in je in ɗauke shi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ عِيسَىٰ يَتَمْبَيٜىٰتَ يَثٜىٰ «عُوَرْغِدَا، مٜىٰيَسَا كِكٜىٰ كُوكَا؟ وَ كِكٜىٰ نٜىٰمَ؟» تَنَ ڟَمَّنِ كُواْ شِينٜىٰ مَيْ عَيْكِ أَغُواْنَرْ، شِے يَسَا تَثٜىٰمَسَ «مَيْغِدَا، إِنْ كَيْنٜىٰ كَطَوْكٜىٰشِ، غَيَ مِنِ عِنْدَ كَسَا شِ مَنَ دُوانْ إِنْ طَوْكٜىٰشِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Yesu ya ce mata, “Uwargida, don me kike kuka? Wa kuma kike nema?” Saboda kuma ta zaci shi ne mai aikin lambun, ta ce masa, “Maigida, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka sa shi mana, ni kuwa in ɗauke shi.”