John 21:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za tă sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَݣَويْ وَطَنْسُ أَبُبُوَ دَيَوَ كُمَ وَطَنْدَ عِيسَىٰ يَيِ دَاعَثٜىٰ ذَاعَ رُبُوتَ دُكَ، إِنَ ڟَمَّنِ كُواْ دُونِيَا كَنْتَ بَذَاتَ عِيَ طَوْكَرْ لِتَّتَّڢَنْ دَ ذَاعَ رُبُوتَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Akwai waɗansu al'amura kuma masu yawa da Yesu ya aikata, in da za a rubuta kowannensu ɗaya ɗaya da ɗaya ɗaya, ina tsammani ko duniya kanta ba za ta iya ɗaukar littattafan da za a rubuta ba.