John 4:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai mutuniyar Samariyar ta ce masa, “Kai mutumin Yahuda ne, ni kuwa mutuniyar Samariya ce. Yaya za ka roƙe ni ruwan sha?” (Don Yahudawa ba sa hulɗa da Samariyawa.)
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مَثٜىٰنَّنْ بَسَمَرِيَ تَثٜىٰ وَ عِيسَىٰ «يَيَ كَيْ بَيَهُودٜىٰ ذَاكَ ضُواْڧٜىٰنِ ضُوً شَا، نِے دَ نَكٜىٰ مَثٜىٰ دَغَ سَمَرِيَ؟» غَمَا يَهُودَاوَا بَاسَ حَطَ عِدُواْ دَ سَمَارِيَاوَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Basamariyar ta ce masa, “Ƙaƙa kai Bayahude za ka roƙe ni ruwan sha, ni da nake Basamariya?” (Don Yahudawa ba sa cuɗanya da Samariyawa).