John 6:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka suka tattara su suka kuma cika kwanduna goma sha biyu na gutsattsarin burodin sha’ir biyar nan da suka ragu bayan kowa ya ci.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ أَلْمَجِرَنْ سُكَ تَتَّارَ غُڟَڟَّرِنْ غُرَاسَرْ سُكَ ثِكَ ݣُونْدُنَ غُواْمَشَا بِيُ، وَتُواْ غُڟَڟَّرِنَّنْ دَغَ دُنْڧُلٜىٰنْ غُرَاسَ بِيَرْ نَبَلٜىٰ نَنْ وَطَنْدَ سُكَ ضَغٜىٰ بَايَنْدَ مُتَنٜىٰ سُكَثِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka tattara gutsattsarin gurasar nan biyar na sha'ir da suka saura bayan kowa ya ci, suka cika kwando goma sha biyu.