John 6:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kashegari taron da suka tsaya a wancan ƙetaren tafkin suka lura cewa jirgin ruwa ɗaya ne yake a can dā ma, kuma sun lura cewa Yesu bai shiga ciki tare da almajiransa ba, gama sun tashi su kaɗai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ غَرِ يَوَايٜىٰ سَوْرَنْ مُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰ ظَوْنٜىٰ عَڧٜىٰتَرٜىٰنْ تٜىٰكُنْ سُكَ لُورَ ثٜىٰوَ دَا مَا جِضْغِ طَيَ نٜىٰ كُرُمْ يَذُواْ وُرِنْ، سُكَ كُمَ لُورَ عِيسَىٰ بَيْ شِغَ ثِكِنْ جِضْغٍ تَرٜىٰدَ أَلْمَجِرَنْسَبَ، أَلْمَجِرَنْسَ نٜىٰ كَطَيْ سُكَ تَڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kashegari sauran taron da suka tsaya a hayin tekun suka lura ba wani jirgi a wurin, sai wani ɗan ƙarami, suka kuma lura Yesu bai shiga cikinsa tare da almajiransa ba, sai almajiran ne kaɗai suka tafi.