John 7:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
To, in za a iya yin wa yaro kaciya a ranar Asabbaci don kada a karya dokar Musa, don me kuke fushi da ni saboda na warkar da mutum a ranar Asabbaci?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُواْ، عِدَنْ أَنَ عِيَيِ وَيَرُواْ كَاثِيَ أَ رَانَرْ هُوتُ تَمَكُواْ دُواْمِنْ دَيْ عَيِ بِيَيَّ دَ كُواْيَرْوَرْ مُوسَٰى، تُواْ، مٜىٰيَسَا ذَاكُيِ ڢُشِے دَنِے سَبُواْدَ نَوَرْكَرْدَ جِكِنْ مُتُمْ سَرَيْ أَ رَانَرْ هُوتُ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
To, in ana yi wa mutum kaciya ran Asabar don gudun keta Shari'ar Musa, kwa yi fushi don na warkar da mutum sarai ran Asabar?