John 7:52 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai suka amsa suka ce, “Kai ma daga Galili ne? Bincika ka gani, za ka iske cewa ba annabin da zai fito daga Galili.” [Rubuce-rubucen farko-farko da kuma mafi ingancin da aka fi dogara da su tare da waɗansu shaidu na dā ba su da Yoh 7.53–8.11. Kaɗan daga cikin rubuce-rubucen hannu na dā sun ƙunshi waɗannan ayoyi, ko gaba ɗayansu ko kuma sashensu kawai bayan Yoh 7.36, Yoh 21.25, Luk 21.38 ko kuwa Luk 24.53.]
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سُكَ أَمْسَ مَسَ سُكَثٜىٰ «كَيْ مَا مُتُمِنْ غَلِيلِ نٜىٰ؟ كَبِنْثِكَ رُبُوتَثِّيَرْ مَغَنَرْ اللَّهْ كَغَنِ مَنَ، أَيْ، بَا وَنِ أَنَّبِنْدَ ذَيْذُواْ دَغَ غَلِيلِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka amsa masa suka ce, “Kai ma Bagalile ne? Bincika mana ka gani, ai, ba wani annabi da zai bayyana a ƙasar Galili.” [