Jonah 1:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai suka yi kuka ga Ubangiji suka ce, “Ya Ubangiji, in ka yarda kada ka bar mu mu mutu saboda ran mutumin nan. Kada ka yi mana hukuncin masu kisankai, gama kai ne, ya Ubangiji, ka ga ya gamshe ka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سُكَيِ كُوكَا غَ يَهْوٜىٰهْ ، اللَّهْ نَ يُونُسَ، سُكَثٜىٰ «يَا يَهْوٜىٰهْ ، مُنَ ضُواْڧُوانْكَ كَدَ كَبَرْمُ مُمُتُ سَبُواْدَ رَنْ مُتُمِنَّنْ؞ كَدَ أَلْحَكِنْ جِنِنْ مَرَرْ لَيْڢِے يَذَوْنَ عَكَنْمُ؞ غَمَا، يَا يَهْوٜىٰهْ ، كَا عَيْكَتَ أَبِنْدَ يَغَمْشٜىٰكَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka yi kuka ga Ubangiji, suka ce, “Ya Ubangiji, muna roƙonka kada ka bar mu mu halaka saboda ran mutumin nan, kada ka yi mana hukuncin masu kisankai, gama kai ne, ya Ubangiji, ka yi abin da ya gamshe ka.”