Jonah 1:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dukan matuƙan jirgin suka tsorata, kowannensu kuma ya yi kuka ga allahnsa, suka kuma jefar da kayan jirgi a cikin teku domin su rage nauyin jirgin. Ana cikin haka, ashe, Yunana ya sauka can ƙarƙashin jirgi ya je ya kwanta, yana ta sharar barcinsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكَنْ مَاسُ تُوڧِنْ جِضْغٍ سُكَجِڟُواْرُواْ، كُواْوَ يَيِ كُوكَا غَ اللَّهْنْسَ؞ سُكَ جٜىٰڢَرْ دَ كَايَنْ دَيَكٜىٰ ثِكِنْ جِضْغٍ عَتٜىٰكُنْ دُواْمِنْ أَ ضَغٜىٰ نَوْيِنْ جِضْغٍ، كَدَ يَنُڟٜىٰ؞ أَنَ ثِكِنْ حَكَ، أَشٜىٰ، يُونُسَ يَارِغَا يَسَوْكَ ذُوَا ثِكِنْ ڧَسَرْ جِضْغٍ يَݣُونْتَ يَيِ بَرْثِ مَيْ ظُرْڢِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukan matuƙan jirgin suka firgita, sai kowannensu ya shiga roƙon allahnsa. Suka yi ta jefar da kayan da suke cikin jirgin a ruwa don su sami sauƙi. Yunusa kuwa yana can cikin jirgi, a kwance, yana ta sharar barci.