Jonah 2:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na nutsa har ƙarƙashin tuddai; a ƙarƙashin duniya, ka rufe ni har abada. Amma ka dawo da raina daga rami, Ya Ubangiji Allahna.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَنُڟٜىٰ ثِكِنْ تٜىٰكُ حَرْ غِنْدِنْ دُوَڟُو، أَنْكُلّٜىٰنِ ثِكِنْ وُرِنْ ذَمَنْ مَتَتُّو؞ عَمَّا، كَيْ يَا يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نَا، كَا ڢِتَرْ دَنِے دَغَ وَنَّنْ رَامِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na tafi can ƙasa ƙarƙashin tussan duwatsu. Ƙasar da ƙofarta take rufe har abada, Amma ka fitar da ni daga cikin ramin, ya Ubangiji Allahna.