Jonah 3:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ya yi umarni a Ninebe cewa, “Bisa ga umarnin sarki da fadawansa. “Kada a bar wani mutum ko dabba, garke ko shannu, su ɗanɗana wani abu; kada a bari su ci ko su sha.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے يَسَا عَكَيِ شٜىٰلَ أَ نِنٜىٰبَ ثٜىٰوَ «عُمَرْنِ نٜىٰ دَغَ وُرِنْ سَرْكِے دَ مَنْيَنْ مُتَنٜىٰنْ بِرْنِ؞ كَدَ مُتُمْ، كُواْ دَبَّ، كُواْ غَرْكٜىٰنْ شَانُو، كُواْ نَتُمَكِ يَطَنْطَنَ وَنِ أَبُ؞ كَدَ مَا سُثِ كُواْ سُشَا ضُوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya aika wa mutanen Nineba da sanarwa cewa, “Wannan doka ce daga sarki da majalisarsa. Kada kowa ya ci wani abu, mutane, da shanu, da tumaki, da awaki duka, kada kowa ya ci, ko ya sha ruwa.