Jonah 4:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ashe, ba dole ne in ji tausayin babban birnin nan Ninebe mai mutum sama da dubu ɗari da ashirin (120,000) marasa alhaki, da kuma dabbobi masu yawa ba?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَشٜىٰ، نِے كُوَ بَذَنْجِ تَوْسَيِنْ نِنٜىٰبَ بَبَّنْ بِرْنِنَّنْ بَ؟ بِرْنِنْ دَ يَكٜىٰدَ یَنْ يَارَا مَرَسَ أَلْحَكِ ڢِيٜىٰدَ دُبُو طَرِے دَ دُبُو عَشِرِنْ عَثِكِنْسَ؟ كَيْ! بَنْدَ مَا دَبُّواْبِنْ دَسُكٜىٰ عَثِكِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ashe, dole ne ni kuma in ji tausayin Nineba, babban birni mai 'yan yara fiye da dubu ɗari da dubu ashirin marasa alhaki, da kuma dabbobi masu yawa.”