Joshua 1:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ku ratsa cikin sansani, ku gaya wa mutane, ‘Ku shirya guzurinku. Nan da kwana uku za ku ƙetare Urdun a nan, don ku je ka mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ta zama taku.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُشِغَ ثِكِنْ مُتَنٜىٰ سُبَاسُ وَطَنَّنْ عُمَرْنَيْ؞ سُثٜىٰ «كُشِرْيَ وَكَنْكُ عَبِنْثِ دُواْمِنْ عَثِكِنْ ݣُونَ عُكُ ذَاكُ ڧٜىٰتَرٜىٰ كُواْغِنْ يُواْدَنْ دُواْمِنْ كُشِغَ ڧَسَرْدَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ يَكٜىٰ بَاكُ كُغَاجٜىٰتَ كُكُمَ مَلَّكٜىٰتَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ku shiga zango, ku umarci jama'a, ku ce, ‘Ku shirya wa kanku guzuri, gama nan gaba da kwana uku za ku haye Kogin Urdun don ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.’ ”