Joshua 1:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
har sai lokacin da Ubangiji ya ba su hutawa, kamar yadda ya yi muku, kuma har sai su ma sun ƙwace ƙasar da Ubangiji Allahnku ya yi alkawari zai ba su. Bayan haka ne za ku koma ku mallaki ƙasarku, wadda Musa bawan Ubangiji ya ba ku a gabashin Urdun.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكُ تَيْمَكٜىٰسُ حَرْ سَيْ لُواْكَثِنْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَبَا یَنْعُوَنْكُ هُوتُ كَمَرْ يَدَّ يَبَاكُ، سُكُمَ مَلَّكِ ڧَسَرْدَ تَكٜىٰ يَمَّ دَ يُواْدَنْ، وَدَّ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ يَكٜىٰبَاسُ؞ بَايَنْ وَنَّنْ، ذَاكُ عِيَ كُواْمُواْوَ كُذَوْنَ عَثِكِنْ ڧَسَرْكُ دَتَكٜىٰ غَبَسْ دَ يُواْدَنْ، وَدَّ مُوسَٰى بَاوَنْ يَهْوٜىٰهْ يَبَاكُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
har lokacin da Ubangiji ya hutar da 'yan'uwanku kamarku, su kuma su mallaki ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba su, a sa'an nan za ku koma zuwa ƙasar da take mulkinku, ku mallake ta, wato ƙasar da Musa, bawan Ubangiji, ya ba ku a hayin Urdun wajen gabas.”